Ko sojojn Koriya ta Arewa na taya Rasha yaƙi a Ukraine? - BBC News Hausa (2024)

Ko sojojn Koriya ta Arewa na taya Rasha yaƙi a Ukraine? - BBC News Hausa (1)

Asalin hoton, Reuters

Bayani kan maƙala
  • Marubuci, Ilya Abishev
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Russian

Ana samun ƙarin rahotanni da ke cewa ana kai sojin Koriya ta Arewa Rasha domin taya ta yaƙi da makwabciyarta Ukraine. A makon da ya wuce kamfanonin dillancin labaran Ukraine na Interfax-Ukraine da KyivPost, suka rawaito wata majiya a hukumar leƙen asirin ƙasar na cewa ranar 3 ga watan Oktoba, an kashe sojojin Koriya ta Arewa shida da jikkatar wasu uku lokacin da makamai masu linzamin da Ukraine ta harba wa Rasha suka faɗa sansanin da sojojin ke atisaye a yankin Donbas da Rasha ta mamaye.

Kamar yadda majiyar ta bayyana, tawagar sojojin Koriyar sun je don ganawa da takwarorinsu na Rasha domin musayar bayanai da kwarewr aiki. Sai dai abin tambayar a nan shi ne, hakan ta faru?

Bayanan sirri da Ukraine ta ruwaito a bara, sun ce wata karamar tawagar sojin Koriya, musamman fannin injiniyoyi sun iso yankin Ukraine da Rasha ta mamaye, sai dai har yanzu Rashar ba ta ce uffan kan wannan iƙirarin ba.

A ranar 8 ga watan Oktoba ministan tsaron Koriya ta Kudu Kim Yong-hyun, ya ce akwai yiwuwar Koriya ta Arewa ta tura sojinta zuwa Rasha.

Ya yi amannar cewa ta yi wu batun kashe sojojin Arewa a yankin Donbas gaskiya ne.

''Tun bayan da Rasha da Koriya ta Arewa suka rattaɓa hannu kan wata yarjejeniyar haɗin gwiwa ta aikin soji, ake batun wataklila a tura sojin Arewar don taimakawa na Rasha,'' yana magana ne akan yarjejeniyar watan Yunin da ya wuce tsakanin shugaba Kim Jong-un da Vladimir Putin na Rasha.

A watan Yunin shekarar nan, lokacin da Putin da Kim suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da ta kun shi fahimta kan aikin soji, an kuma tambaye shi a lokacin ko za a iya ganin sojin Arewa a Ukraine.

''Babu wanda ya tuntuɓe mu kan hakan, kuma ba na jin akwai mai aniyar hakan,'' wannan ce amsar da shugaba Putin ya ba da.

Ƙaruwar haɗin kai

Ko sojojn Koriya ta Arewa na taya Rasha yaƙi a Ukraine? - BBC News Hausa (2)

Asalin hoton, Reuters

Dukkan ƙasashen biyu dai na ƙoƙarin lulluɓe batun tura sojin Koriya ta Arewa yaƙi da Ukraine.

A watan Yuli 2023, ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu, ya yi balaguro zuwa Pyongyang, babban birnin Koriya ta Arewa, don yaukaka dangantakar soji tsakanin ƙasashen biyu, kamar yadda kafar yaɗa labaran Rasha ta bayyana a watan Satumba lokacin da Kim Jong-un ya kai ziyara Rasha.

A watan Satumba 2023 a jawabin da ya gabatar gaban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol, ya yi shaguɓe kan yiwuwar Koriya ta Arewa ka iya sayar wa Rasha makamai da taimakon fasahar zamani.

Ranar 16 ga watan Oktoba 2023, cibiyar tsaro ta Birtaniya ta fitar da wani rahoton cewa Rasha ta karɓi wasu makamai da suka fito daga Koriya ta Arewa.

Rahoton ya nuna hotunan wasu daga cikin makaman, sai dai mai magana da yawun fadar Kremlin Dimitry Peskov ya yi watsi da rahoton.

"Ba fa kwararrun Birtaniya ne kaɗai suka ba da bayanan ba, akwai na Amurka, duka sun ba da rahoton a lokaci guda, amma babu wata kwakkwarar shaida ta tabbatar da hakan,'' in ji Peskov.

Sai dai zuwa karshen shekarar 2023, alamu sun bayyana na yadda ake amfani da makaman Koriya ta Arewa a yaƙin da Rasha ke yi da Ukraine, kuma manyan sojin Rashar sun yi tattaunawar sirri kan hakan.

Ko sojojn Koriya ta Arewa na taya Rasha yaƙi a Ukraine? - BBC News Hausa (3)

Asalin hoton, Reuters

A watan Janairun 2024, kakakin zauren kwamitin tsaro na Amurka John Kirby, ya ce makamai masu linzami da ke cin dogon zango da Rasha ta yi amfani da su a kai hari Ukraine mallakin Arewa ne.

Rahotanni sun ce Koriya ta Arewa na shirin aika sojojinta injiniyoyi, jim kaɗan bayan ziyarar da shugaba Putin ya kai, wanda shi ma ya yi tasiri kan yaɗa jita-jitar.

Hakan ya sanya Dimitry Peskov ya maida martani da cewa; 'Ban san abin da wannan ke nufi ba, jita-jita ce kawai.''

'Yan jarida da kafafen yaɗa labarai da dama sun tuntuɓi ofishin Mista Peskov domin yin cikakken bayani kan makasudin ziyarar da Putin ya kai wa Kim, amma sai ya ce su tuntuɓi ma'aikatar tsaron Rasha kan hakan.

Me muka sani kan sojojin Koriya ta Arewa?

Ko sojojn Koriya ta Arewa na taya Rasha yaƙi a Ukraine? - BBC News Hausa (4)

Asalin hoton, Reuters

Za a iya cewa ba a samun bayanai da suka shafi rundunar sojojin Koriya ta Arewa, komai cikin sirri ake yin shi, abu ɗaya da za a iya gani a zahiri shi ne yawansu.

Ƙasar na ɗauke da sojoji maza da mata, kuma tilas ne ga 'yan ƙasa su yi aiki da rundunar sojin Koriya ta Arewa na aƙalla shekara uk zuwa goma, ya kuma danganta da inda aka kai mutum horo.

Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2018, ya nuna Koriya ta Arewa ce ta huɗu a duniya mai yawan sojoji, inda suka kai kusan miliyan 1.2.

Wani kwararre a Rasha mai suna Andrei Gubin, ya ce watakil adadin ka iya yin yawa, ''A halin yanzu dai akwai kididdigar da ake da tabbacin sojojin Koriya ta Arewa su kai 850,000, sai kuma wani kiyasin da aka yi na sojojin da ke aiki na dindindin da suka kai 650,000.''

Ya bayyana hakan ne a wata maƙala da ya rubuta kan shirin sojin Koriya ta Arewa.

Ya ƙara da cewa akwai sama da 'yan ƙasar miliyan huɗu da ke jiran lokacin da za a tura su horo, sannan baki-ɗaya idan aka haɗe dukkan sojojin daga fannoni daban-da ban, za su kai sama da miliyan shida.

Zai yi wuya a ce ana ɓoye-ɓoye kan hakan

Tsari da horon sojojin Koriya ta Arewa na tafiya ne kan tsarin tarayya da horon sojin Serbia, ba kamar sojojin Rasha ba da ba su da kwarewa ta fannin yaƙi.

Har yanzu babu tabbacin irin rawar da za su taka a yaƙin da Rasha ke yi a Ukraine, ko za su iya taɓuka abin a zo a gani, sannan dakarunsu na da karfi da jajircewa a gida, ko hakan zai faru a wata ƙasar?

Shin za su yi aiki a karamar tawaga? Wanda zai buƙaci samar da wata runduna da za ta sanya ido a kan su. Koma yaya ne, abu ne mai matukar wuya aikin sojin Koriya ta Arewa ya ɓuya a Rasha.

Runduna mai arha

Ko sojojn Koriya ta Arewa na taya Rasha yaƙi a Ukraine? - BBC News Hausa (5)

Asalin hoton, Reuters

Duk wannan bayanin ba shi ne zai tabbatar da sojojin Koriya ta Kudu na aiki tare da sojin Rasha a yaƙin da ta ke yi a Ukraine ba.

Abu ɗaya da ya bayyana shi ne, Koriya ta Arewa dai na buƙatar kuɗi da fasahar zamani, ita kuma Rasha na buƙatar sojojn da za su taya ta aiki, don haka za a yi abin nan da ake cewa ban-gishiri-in-baka-manda.

Don haka akwai yiwuwar sojojin Koriya ta Arewa su yi aiki a Rasha kan albashi ɗan kaɗan, kamar yadda aka san sojin ƙasar da aiki kan farashi mai rahusa tun lokacin da ake ƙoƙarin kafa bataliyar tarayyar Sabiya.

Za a iya kai sojin Koriya ta Arewa wasu wuraren a Rasha, misali sake gina ababen more rayuwa na sojoji da aka lalata da sake gina gidajen karkashin ƙasa na ajiyar makamai, da gadoji da kuma manyan hanyoyin da aka lalata.

A ɓangare guda kuma samun sojin Koriya ta Arewa, na nufin Rasha za ta samu damar tura zaratan sojojinta sahun gaba a fagen daga, domin ci gaba da fafatawa da sojin Ukraine.

Ko sojojn Koriya ta Arewa na taya Rasha yaƙi a Ukraine? - BBC News Hausa (2024)

References

Top Articles
Latest Posts
Recommended Articles
Article information

Author: Dan Stracke

Last Updated:

Views: 5711

Rating: 4.2 / 5 (43 voted)

Reviews: 82% of readers found this page helpful

Author information

Name: Dan Stracke

Birthday: 1992-08-25

Address: 2253 Brown Springs, East Alla, OH 38634-0309

Phone: +398735162064

Job: Investor Government Associate

Hobby: Shopping, LARPing, Scrapbooking, Surfing, Slacklining, Dance, Glassblowing

Introduction: My name is Dan Stracke, I am a homely, gleaming, glamorous, inquisitive, homely, gorgeous, light person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.